Safna Aliyu Maru daya ce daga cikin Jarumai mata da tauraruwarsu take haskawa, a masana’antar fina-finan Hausa. Domin kuwa ta yi finafinai masu yawa daga lokacin da ta shigo masana’antar zuwa wannan lokaci, dadin-dadawa ma Jarumar ta samu damar shirya fim na kanta har guda biyu. Domin jin ko wace ce jarumar, wakilinmu ya tattauna da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:
Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.
Assalamu alaikum, ni dai sunana Safna Aliyu Maru kuma ni haifaffiyar Kano ce, mahaifiyata ‘yar Kano ce. Babana ne dan asalin garin Maru ta jihar Zanfara, kuma an haife ni a 1993 na yi makarantar firamare a Giginyu, na yi sakandire a Badawa a yanzu kuma ina ci gaba da karatu a Kwalejin Koyon Shari’ar Musulunci ta Aminu Kano.
Me Ya Sa Kika Fara Fim, Alhali Kina Karatu?
Na shiga harkar fim a 2014 kuma dalilin shigowa ta fim saboda yadda harkar take burge ni a game da abubuwan da ake gudanarwa na fadakarwa da nishadantarwa. Don haka ne sai na je na nemi shawarar iyaye na su kuma suka bani dama.
A lokacin da kika zo da wanne fim kika fara.?
Na fara ne da fim din ‘Wani Dare,’ wanda kuma ni ce Jarumar fim din, daga nan ne sai ‘Zulaihat’ shi ma ni ce na fito a matsayin Jarumar fim din.
Daga lokacin da kika fara zuwa yanzu kin yi fina-finai kamar nawa?
E, to na yi fim kamar guda talatin sai dai ba zan iya fadar su duka ba, amma zan iya fada maka wasu daga cikin su kamar: ‘Wani Dare,’ ‘Zulaihat,’ ‘Fuska Biyu,’ ‘Daren Zalunci,’ ‘‘Yan Makaranta’ sai kuma ‘Kukan Kurciya.’
To, cikin fina-finan da kika yi wanne kika fi ji da shi?
Gaskiya na fi ji da ‘Fuska Biyu’ saboda shi fim di na ne da na zuba kudi na na shirya don haka nake ji da shi.
Sauda dama Jarumai idan sun shigo harkar fim sukan dauki lokaci kafin a ba su wani rol mai karfi, amma ke kamar yadda kika fada daga shigowarki fim dinki na farko da na biyu ke ce ki ka zamo jarumarsu ko mene ne sirrin wannan nasara.
Ka san akwai labarin da zai zo wanda shi kaga sabuwar fuska ake bukata ta hau rol din ina ganin hakan ce ta sa, kuma dai idan mutum ya shigo da sa’a dai hakan take faruwa.
Duk wanda ya shiga masana’antar fim a kan sami wani buri da yake da shi ke wane buri kike da shi? Kuma kin kai ga nasara ko dai da saura?
To na yi godiya ga Allah ina da buri kuma zan iya cewa na kai ga cin nasara ko kuma ina kan hanya domin ni daman ina son na zama Furodusa. Sannan ina so na yi Daraktin, to yanzu na zama Furodusa ka ga ina kan hanya kenan.
Kasancewar ki a cikin manyan Jarumai masu tasowa, yaya za ki kwatanta rayuwarki ta harkar fim?
Rayuwar Industiri tana da dadi kuma takan canza maka yana yin rayuwarka ta baya, domin a baya mutane da ‘yan’uwan ka za su zo gida ku zauna ku yi ta hira, amma yanzu babu lokaci yau kana nan, gobe kana can don haka rayuwarka sai ta canza ya zama ba ka da lokaci kamar a baya.
To yaya kike samun kan ki idan kin shiga cikin taron mutane ko a Kasuwa in kin je yin sayayya?
Ka san shi dan fim duk inda yake yana da farin jini don haka duk inda na samu kai na a cikin jama’a zan ji mutane suna cewa wance ce ta zo sai ka ga sun zo muna gaisawa muna yin hotuna suna jin dadi. Kaima kana jin dadi da farin ciki.
A wani lokaci masu kallo sukan kalli Jarumi da rol din da ya taka a cikin fim, kin taba samun haka ga masu kallon ki?
Ka san ni yawanci rol din da ake ba ni na abin tausayi ne don haka masu kallo suna kallo na da wannan yana yin don haka ba na samun wata tsangwama daga gare su sai dai a rinka kallo na abin tausayi saboda halin da ake gani na a cikin fim don haka bana samun matsala.
A cikin fina-finan da kika yi wanne ya fi wahalar da ke?
Gaskiya ‘Kukan Kurciya’ shi ne ya fi wahalar da ni, ban taba yin fim din da ya wahalar da ni kamar sa ba. Saboda a cikin daji aka yi fim din, an yi gudu har na fadi. Sannan fim na biyu da shi ma ya wahalar da ni shi ne ‘Wata Rana’ shi kuma fim dina ne da na yi a kwanannan shi ma dai a dajin ake yin aikin.
Akwai wani abu da kika taba yin da na sanin sa a har kar fim?
To, gaskiya a yanzu babu wani abu da na yi nake yin da na sanin sa a harkar fim kuma ba na fata nan gaba ma na yi shi.
Yanzu dai za mu iya cewa Safna ba ta da wani buri a gabanta?
Ai dan adam ba ya rasa buri a rayuwar sa, yanzu burin da yake gabana shi ne na samu miji na yi aure na bar harkar fim lafiya kamar yadda na shigo lafiya.
Bayan harkar fim akwai wata harka da kike yi wadda ta shafi kasuwanci na sana’a?
Sosai ma kuwa ina yin harkar kasuwanci domin ina sayar da kayan mata irin su Atamfa, Leshi da sauran kayayyaki irin su Jakunkuna harda shaddoji na maza.
Wanne albishir kike da shi ga masoyanki, a karshe, musamman masu kallo?
To, ni dai babu abin da zan ce ga masoya na sai dai na yi musu fatan alheri, kuma idan sun ga na yi wani abu da ya bata musu rai su yi hakuri ba da niyya na yi ba. Kuma idan sunga ba sa gani na a fim to yana yin karatu ne da nake yi ga kuma harkokin kasuwanci na don haka za su rinka gani na kadan-kadan a fina-finai daga karshe dai ina yi wa kowa fatan alheri.
Tura wannan zuwa ga shafukan sadarwa domin Yan Uwa da Abokai.
0 Response to "(Tattaunawa) Minti Biyar Da Safna: Tarin Nasarorin Da Ta Samu A Harkar Film"
Post a Comment