Tsohon shugaban FIFA Joao Havelange ya rasu wanda ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24

Wasu ‘Yan wasan ninkayar Amurka da aka tsare a Brazil kar zargin cewar an yi mu su fashi sun bar kasar bayan sun amsa cewar karya suka yi. Hukumomin ‘Yan Sandan Brazil sun tsare ‘Yan wasan biyu inda suka gudanar da bincike wanda ya nuna cewar babu wanda ya mu su fashi.

Shugaban hukumar wasan Olympics an Amurka Scott Blackmun ya nemi gafarar Brazil kan abin da ya faru.

Batun dai ya mamaye kanun labarai a wasannin Olympics na Rio bayan ‘Yan wasan ninkayar Amurka hudu sun ikirarin cewa an tare su da bindiga a wani gidan sayar da mai a Rio a ranar Lahadi.

Tuni kuma biyu daga cikinsu suka bar Brazil suka koma gida sakamakon bacin sunan da suka janyo wa Amurka.

KARIN LABARAI
european football news
 
Tsohon shugaban FIFA Joao Havelange ya rasu wanda ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24 tsakanin 1974 zuwa 1998. Ya rasu ne a cibiyar shi birnin Rio na Brazil yana da shekaru 100 a duniya.

Sepp Blatter ne ya gaje shi wanda ya kasance shugaban FIFA na farko da ya fito daga wata nahiya sabanin Nahiyar Turai.

Ya taka rawa sosai wajen inganta harakar kwallon kafa a duniya, kamar yadda Shugaban FIFA na yanzu Gianni Infantino ya ce Havelange ya cancanci yabo a duniyar tamola.

Havelange dan wasan iyon ruwa ne wanda ya taba wakiltar Brazil a wasannin Olympics da aka gudanar a Berlin a shekarar 1936.

Ya taba zama cikin kwamitin shirya wasannin Olympic.

Yanzu haka kuma sunan shi aka saka a filin wasan Olympics a Rio daya daga cikin wuraren da ake wasannin a Rio a bana.

Shugaban kwamitin Olympics Thomas Bach ya ce za a sassauta tuta a filayen wasannin na Rio saboda rasuwar Havelange.

0 Response to "Tsohon shugaban FIFA Joao Havelange ya rasu wanda ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24"

Post a Comment